An danganta raguwar namun daji da bautar da yara

Hakkin mallakar hoto no credit

Wani sabon bincike ya nuna cewa raguwar namun daji a duniya nada alaka da karuwar safarar biladama da kuma bautar da yara kanana

Masu binciken sun ce karancin namun daji na nufin a kasashen da dama yanzu ana bukatar karin aikin kwadago domin neman abinci

Akan yi amfani da Yara kanana domin wannan bukatar musamman a bangaren kamun kifi

Raguwar dabbobi yana kuma taimakawa wajen bazuwar ayyukan ta'addanci da kuma tabarbarewar yankuna

Kamar yadda wani bincike a wata mujalla ta Kimiyya ya nuna, ana samun biliyan $400 a shekara a kama namun daji daga teku da kuma a kasa kuma yana samar da hanyar abinci ga kashi 15% na al'ummar duniya

Amma masu wallafa binciken sun ce raguwar namun dajin yasa ana bukatar karin ayyukan bauta.

Hakkin mallakar hoto f

Raguwar kifi a daukacin duniya na nufin a wsau lokuta dole ne kwale kwale ya yi tafiya mai nisa karkashin yanayi maras kyau domin neman kifin da za a kama

A yankin Asiya, maza daga Kasashen Burma da Cambodia da Thailand na kara sayar da jiragensu na kamun kifi bayan sun zauna a teku shekara da shekaru ba tare da samun kudi ba, da kuma tilasta masu yin aiki na sa'oi 18-20

Al'ummomi da dama da suka dogara da namun daji basu da karfin tattalin arzikin da zasu yi hayar karin leburori, a saboda haka suke neman ma'aikatan kwadago masu arha kuma a yankuna da dama hakan ya haifar da cinikin kananan yara a matsayin bayi

Wannan lamari na faruwa a Afirka inda mutane wadanda a wani lokaci suke samun abincinsu a dazuka dake makwabtaka da su, a yanzu suke tafiya mai nisa domin neman abinda zasu ci