Al Zakzaky ya rasa 'ya'yansa 3 a muzahara

Image caption 'Yan uwa musulmi mabiya mazhabar shi'a sun gudanar da mazahara a ranar Jumu'a a Zaria

A Zaria dake jahar Kadunan Nigeria kimanin mutane 13 ne suka rasu wasu kuma da dama suka sami raunuka a yayin da wasu wadanda ake zargin Sojoji ne suka bude wuta akan kungiyar 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar Shia bayan sun kamala muzaharar ranar Palasdinawa a ranar jumu'a.

Shugaban kungiyar 'yan uwa musulimin Sheik Ibrahim Alzakzaky ya tabbatarwa da BBC cewa ya rasa 'ya'yan sa a cikin wannan hari.

Al Zakzaky ya yi zargin cewa sojoji ne suka budewa 'yan uwa musulmi wuta bayan kammala mazahara a ranar jumu'a.

Har yanzu dai jami'an Soji ba su ce komai ba dangane da zargin cewa Sojoji ne suka kaddamar da harin.