Isra'ila ta tsawaita tsagaita wuta

Hakkin mallakar hoto AP

Gwamnatin Isra'ila ta tsawaita tsagaita wutar wucin gadin da aka cimma a Gaza da sa'o'i 4 ya zuwa tsakiyar dare a agogon can.

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta sa'o'i 12 da dukanin Isra'ilar da kungiyar Palasdinawa ta Hamas suka tabbatar a jiya Juma'a ta kare.

Hamas ba ce ko ya Allah za ta tsawaita yarjejeniyar, ko kuma a'a ba.

Sai kuma, dan lokaci kadan da ya wuce, sojin Isra'ila sunce an harba rokoki 3 daga Gaza, kuma sun dira cikin Isra'ila.Babu wanda ya samu rauni ko ya mutu.

Palasdinawa dubu daya ne aka kashe tun lokacin da rikicin ya soma, Yan Israila fiye da 40 -- galibi sojoji suka mutu suma.

Karin bayani