Sallah: An hana zirga zirgar motoci a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Maiduguri na fuskantar hare haren kungiyar Boko Haram

Wata sanarwa ta jami'an tsaro a Maiduguri ta hana zirga zirgar motoci a garin Maiduguri na tsawon kwanaki uku daga ranar litinin.

Rundunar tsaron sojojin ta ce ta samu rahotannin da ke cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun shirya kai hare-hare a birnin shi ya sa ta dauki wannan mataki.

Sai dai wasu mazauna garin na Maiduguri sun nuna damuwa game da takaita zirga zirgar motocin

Birnin Maiduguri dai na fama da hare haren 'yan kungiyar Boko Haram.