Mutum-Mutumi sun zama 'yan kallo a Korea

Mutum-Mutumi 'yan kallon wasa a Korea Hakkin mallakar hoto HANWHA EAGLES
Image caption Mutum-Mutumi 'yan kallon wasa a Korea

Kungiyar 'yan wasan kwallon hannu da ake bugawa da kulki watau baseball ta Korea ta kirkiro wata hanya ta zuga 'yan wasan ta a gasar wasa ta hanyar kawo mutumin-mutumi da yawa da aka jera a matsayin 'yan kallo.

Magoya bayan kungiyar 'yan wasan ta Hanwha da ba su samu damar zuwa dandalin wasan ba, za su iya tafiyar da mutum-mutumin ta internet.

Mutumin-mutumin dai suna iya yin sowa ta nuna goyon baya, za su kuma iya rera waka da daga hannaye irin na 'yan Mexico - to amma ba za su iya mamaye filin wasan ba.

Wani kwararre ya ce bayar da dama ga karin wasu 'yan kallo magoya baya su halarci dandalin wasan yana da muhimmanci ga kwararrun kungiyoyin wasa.

Wannan musamman ya fi kasancewa ne ga manyan kungiyoyin wasa na kwallon kafa kamar yadda Matt Cutler editan SportBusiness International ya gaya ma BBC.

Yace, "idan ka kalli manyan kungiyoyin wasa, ba za ka samu tikitin ganin wasan ba na kakar wasanni - dole sai ka bi layi ka jira wasu da suka riga ka neman tikitin."

"Akwai kuma yiwuwar ba da damar sanya tallace-tallace. Za ka iya neman a biya kudi, ko da kuwa kudin kadan ne, domin baiwa 'yan kallo damar kallon wata tashar.".

John Hemmingham wani mai sha'awar kwallon kafa, wanda ke tafiyar da shahararriyar tashar nan ta magoya bayan Ingila, shi kuma ya kalli lamarin ne ta wata fuskar.

Yace, "to idan wani mutum-mutumin dan kallo ya nuna halin banza fa ?" ya yi murmushi.

"idan ya fusata, ko ya baci wani, ko ya fancala wani abin sha fa ... Ina ganin akwai hadari. Idan kuma ya zauna cikin rukunin mutanen da ba na shi ba ne fa ? Ya zama tsageran mutum-mutumi kenan !

Karin bayani