Babu hawan sallah saboda tsaro

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rashin tsaro zai hana hawan Sallah a bana

A Najeriya bukukuwan Salla a bana zasu gamu da cikas saboda matsalar tabarbarewar tsaro.

A bana akasarin masarautun arewacin kasar ba za su gudanar da al'adar nan ta hawan Sallah ba sakamakon rashin tsaro.

Kuma tuni wasu masarauntun suka ba da sanarwar cewa ba za su yi hawan Sallar ba tun a ranar Asabar bayan sanarwar ganin watan Sallar.

Masarautar Kano da ta Daura na daga cikin masarautun da ba za a yi hawan Sallar ba.

Alhaji Aminu Ado Bayero wanda yai magana a madadin masarautar Kano ya ce a bana ba za'a yi hawan Sallah ba

Shima Dan Madamin Daura Alhaji Abdurrahman Dan Malan ya shaidawa BBC cewa hare haren da aka kaiwa Janar Muhammadu Buhari da kuma Malamin addinin musuluncin nan Sheikh Dahiru Bauchi sun girgiza su matuka.

A don haka yace ba suga dalilin yin shagulgula ba.

A shekarun baya dai akan gudanar da hawan sallah inda Sarakuna kan zagaye gari suna karbar gaisuwa daga jama'a a cikin wani yanayi na kade-kade da bushe-bushe da kuma annunshuwa.

Ba shakka rashin hawan Sallar ba zai yiwa jama'a da dama dadi ba.