Yau take sallah a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Lahadi take sallah

A Nigeria Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar ya sanar da cewa an ga watan Shawwal a wasu birane na Najeriya.

A don haka ya sanar da cewa Lahadi 27 ga watan Yuli ce ranar Sallah Karama.

Wasu daga cikin biranen da aka ga watan na Shawwal sun hada da Daura da Borno da Talatar Mafara da Zazzau da Adamawa da Minna da kuma wasu bangarori na Sokkoto.

Tuni dama gwamnatin Najeriya ta bayyana Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu.

A sakonsa na taya al'ummar musulmi murna, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi fatan cewa musulmi za su yi amfani da irin kyawawan darussan da suka koya a cikin azumin watan Ramadan wajen cigaba da gudanar da harkokin rayuwar su.

Shugaban ya kuma nuna damuwa game da kalubalen tsaron da ake fuskanta a cikin kasar, inda ya bukaci jama'a da su cigaba da baiwa jami'an tsaro goyan bayan a kokarin da ya ce gwamnatinsa take na yaki da ta'addanci.

Shima a nasa sakon taya murnar kammala azumin watan Ramadanan, Kakakin majalisar wakilan Nigeria Hon. Aminu Waziru Tambuwal ya kuma bukaci 'yan Najeriya da su kiyaye lafiyarsu, yana mai cewa barkewa cutar Ebola a wasu kasashe dake makwabtaka da Najeriyar wata babbar damuwa ce ga kasar.