Kwamitin Sulhu ya nemi dakatar da fada

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Isreala tana amfani da zalincin da ya wuce kima a kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.'

Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya yayi kira da a dakatar da bude wuta kai tsaye, ba kuma tare da wani sharadi ba a Gaza.

A wata ganawa da ya yi cikin dare, a New York, kwamitin ya amince da wani kudiri, da ke bukatar Israela da Hamas da su yi kokarin cimma yarjejeniya mai dorewa ta tsagaita wuta, da za ta bayar da dama a kai kayan agaji ga fararen hula da fadan ya rutsa da su.

A jiya Lahadi, bangarorin biyu sun kara kaimi wajen kai hare-hare, inda kowanne ke zargin dayan da saba yarjejeniyar wucin gadi ta tsagaita wuta.

Jakadan diflomasiyya na Palasdinawa a Birtaniya, Manuel Hassassian, ya gaya wa BBC cewa, Hamas a shirye take ta amince da shawarar dakatar da bude wuta

Ya ce, '' Idan Isreala ta dakatar da kai hare-hare ta sama da kisan kan mai-uwa-da-wabi, ina ganin Hamas za ta saka hakan.''

Karin bayani