Libya: Wuta ta tashi a rumbun mai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An harba makamin ne a lokacin musayar wuta tsakanin kungiyoyin mayakan sa-kai da ke gaba da juna.

'yan kwana-kwana suna fafutukar kashe gaggarumar gobara da ta tashi, bayan wani makamin roka ya fada kan, wani katoton rumbun mai, a babban birnin Libya, Tripoli.

Rumbun, wanda daya ne daga cikin ire irensa da dama da ke cibiyar adana mai ta kamfanin mai na Libyan, yana dauke da man da yawansa ya kai lita miliyan shida.

Wani mai magana da yawun kamfanin ya ce, idan wutar ta yadu zuwa sauran rumbunan da ke wurin, za a samu mummunar bannar da za ta shafi da'irar kilomita biyar.