Libya: Kazamin fada ya barke a Benghazi

Birnin Benghazi na kasar Libya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Birnin Benghazi na kasar Libya

Kazamin fada tsakanin sojin Libya da 'yan gwagwarmayar Islama yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da talatin a birnin Benghazi na gabacin kasar.

Fadan ya hada da jiragen yakin gwamnati da suka jefa bama bamai a wuraren da kungiyar Ansar al Shari'a ke rike da su.

Ana ci gaba da harbe harbe nan da can a Tripoli babban birnin kasar, yayinda Libya ke ci gaba da fuskantar tashin hankali mafi muni tun yakin 2011 da ya hambarar da Muammar Gaddafi.

A ranar Asabar Amurka ta kwashe ma'aikatanta a ofishin jakadancinta da ke Tripoli, yayinda artabu ya kaure a kusa da ginin

Karin bayani