Masu Broadband sun yi watsi da matatar batsa

Wani mai amfani da Internet Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wani mai amfani da Internet

Mafi rinjayen masu amfani da hanyar sadarwar nan mai saurin gaske ta Internet watau Broadband a Brittaniya suna kin yarda su sanya wani matacin dake hana shigar hotunan batsa a Komputar su - wadda aka kira "Child friendly filter" a duk lokacinda kamfanonin sadarwar suka nemi su sanya su a Komputar su.

Kamfanin Ofcom mai sa ido kan harkokin sadarwa a Brittaniya ya gano cewa, cikin gidaje na iyalai bakwai, daya ne kawai za a iya samu wanda ya sanya wannan matacin, wanda kamfanonin sadarwa na BT da Sky da Talk Talk da Virgin Media ke bayarwa.

Shi wannan mataci, yana hana wasu shafuka ne na batsa yin kutse da kuma wasu shafukan dake ingiza mutane su lahanta kawunan su ko tu'ammali da miyagun kwayoyi.

Gwamnatin Brittaniya ce ta nemi kamfanonin su aiwatar da wannan shiri na ba da zabin amfani da matacin a Komputar mutane.

A watan Yuli na shekara ta 2013 Prime Minister David Cameron ya ba da sanarwa cewar manyan kamfanonin sadarwa na Internet a Brittaniyar sun amince za su yi ma abokan huddar su tayin matatar hotunan batsar ga Iyaye wadda ala tilas ne su yi amfani da ita.

Sabbin abokan hulda da kamfanonin suna cin karo da matatar batsar da za ran sun shiga internet, ana kuma tilasta musu da lallai sai sun zabi kin aiki da wannan matatar, idan har ba su son aiki da ita a Komputar su.

To, sai dai kuma rahoton na kamfanin na Ofcom ya gano cewa, masu shiga Internet din suna latsa ficewa daga matatar batsar ne.

Daga cikin manyan kamfanonin sadarwa hudu wadanda kan yi tayin bayar da matacin batsar da za ran sun ga abokan huldarsu sun shiga Internet, kamfanin Talk Talk ne kawai ya iya ciwo kan kashi goma cikin dari na abokan huldarsa suka yarda, suke amfani da matatar batsar a Komputarsu.

Sauran kamfanonin kamar Virgin na da kashi hudu ne cikin dari, yayinda BT ke da kashi biyar, Sky na da kashi takwas, Talk-Talk kuma na da kashi 36 cikin dari na abokan huddar ta sa dake aiki da matacin batsar.

Dukkan wani sabon abokin hulda na kamfanonin sadarwar ta Internet ana yi masa tayin da ake neman sai lallai ya amince da shi, in banda kamfanin sadarwa na Virgin wanda ya gabatar da tayin ga kashi talatin da biyar cikin dari na abokan huldarsa.

Karin bayani