An kubutar da matar Firaministan Kamaru

sojojin kamaru Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun kasar Kamaru

Jami'an tsaro a Kamaru sun kwato uwar gidan Prime Minista Amadou Ali wadda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram suka sace a ranar Lahadi tare da wani basaraken gargajiya na garin Kolofata.

Duk da cewa kakakin gwamnatin kasar minista Issa Tchiroma Bakary na cewa suna kan bincike domin gano addadin rayukan jama'ar da suka hallaka, amma kuma wasu rahotanni na cewa mutane goma sha shida ne suka yi asarar rayukansu a wannan farmaki.

'Yan kungiyar ta Boko Haram dai suna kai farmaki ne a arewacin kasar ta Kamaru inda suke ketarawa daga Najeriya.

Ko a cikin makon da ya gabata wata kotu a kasar ta Kamaru ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 ga wasu 'yan kungiyar su 14 da aka kama da makamai a watan Maris a yankin Marwa da ke arewacin kasar ta Kamaru.

Karin bayani