Bam ya tashi a wani gidan mai a Kano

Image caption Hare-haren bam sun hallake mutane da dama a Kano

Wata mace 'yar kunar bakin wake ta tada bam a wani gidan mai da ke Hotoro a birnin Kano inda ta kashe kanta da kuma wasu mutane uku.

Shaidu sun celamarin ya auku ne yayin da 'yar kunar bakin waken ta shiga cikin mata da suke kan layin sayen kalanzir.

Wannan ne tashin bam na uku cikin sa'o'i 24 a birnin Kano.

Ranar Lahadi, mutane biyar sun rasu sakamakon tashin bam a wani coci.

A wani lamarin daban wata 'yar kunar bakin wake ta kashe kanta lokacin da ta fasa bam a kusa da Northwest ta Kano duk da cewar babu wanda ya rasu sakamakon lamarin.

A wata sabuwa kuma, rundunar 'yan sanda jihar Kano ta ce wata 'yar kunar bakin waken da tada bam a kusada filin bukin baje koli da ke kan titin Zoo inda ta kashe kanta sannan ta raunata mutane shida.