Ukraine: Fada ya hana masu bincike aiki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dangin wadanda suka mutu na fatan ganin an kawo musu 'yan uwansu da kayayyakinsu

Masu bincike na kasashen Holland da Australia sun ce sun kasa isa wurin tarkacen jirgin saman Malaysian nan da ake zargin an harbo a Ukraine, saboda mummunan fadan da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan aware masu goyon bayan Rasha.

Gwamnati ta ce sojojinta na tunkarar yankin da jirgin ya fado, amma kuma, ta musanta cewa suna artabu a dai dai wurin, inda shugaba Petro Poroshenko ya ce masu bincken za su iya aiki.

Shugaban tawagar aikin binciken na Holland, Pieter Jaap Aalbersberg, ya ce sun zaku su fara aikin, amma 'abin takaici ne sai an jira aikin da suka zo su yi.'

Sun samu kwarin guiwa ne daga fatan dangin wadanda hadarin ya rutsa da su daga dukkanin kasashen daban daban, na dawo musu da 'yan uwansu da kayayyakinsu.''