Ebola na barazana ga Birtaniya - Hammond

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Kwayar cutar Ebola mai saurin kisa

Ministan harkokin wajen Birtaniya Philip Hammond ya ce gwamnatin kasar na nazarin annobar cutar Ebola da ta barke a shiyyar Afirka ta yamma, a matsayin wata babbar barazana ga Birtaniya.

Mr Hammond ya yi wani zama da babban kwamitin harkar tsaro don tattaunawa a kan lamarin.

Kungiyar tarayyar Turai dai ta kebe dala miliyon biyu da dubu dari bakwai don taimakawa wajen yaki da cutar.

Sai dai yayin da kasashen duniya da dama ke kokarin daukan matakan kariya, ciki har da yunkurin rufe iyakokinsu, kungiyar agajin likitocin kasa-da-kasa watau 'Doctor Without Borders' ta ce rufe mashigun kasashen ya fi bude su hadari.

Sandra Smiley jami'a ce a kungiyar," Hana wa mutane zirga-zirga za ta maida aiki baya ne a yaki da wannan annobar, saboda wasu mutanen za su koma neman barauniyar hanya, inda za a sha wahala wajen sa ido a kansu."

Mutane fiye da 670 ne suka rasu a Saliyo da Liberia da Guinea da kuma Nigeria tun bayan da cutar ta bulla a cikin watan Fabarairu.