Bam ya kashe mutane uku a Kano

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin da aka kai a makarantar koyon aikin jinya a Kano

Wata 'yar kunar bakin wake ta hallaka kanta da kuma wasu mutane biyu a lokacin da ta tada bam a kofar shiga cibiyar gudanarwa ta makarantun fasaha na Kano watau Kano Polytechnic.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu da rabi na rana a lokacin da dalibai suka taru suna duba sunayen masu tafiya hidimar kasa (NYSC) da aka kafe a wajen.

Wannan ne hari na biyar da aka kai a birnin Kano cikin kasa da kwanaki hudu.

Wani da ke kusa da wajen ya shaidawa BBC cewa ya ga mutane a kwance a kasa, sannan kuma ya ga mutane da dama da suka ji raunuka.

Kimanin mutane 12 ne suka rasa rayukan su a Kanon a wasu hare hare da aka kai ranar Sallah da washe garin Sallah.

Jihar Kano na daga cikin jihohin arewacin Nigeria da 'yan Boko Haram ke kaddamar da hare-hare.