Hijabi: An kashe wata mata a Somalia

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar Al-Shabab na musanta zargin kashe matar

Rahotanni daga kasar Somalia sun ce an harbe wata mata har lahira saboda ta ki sanya hijabi.

Dangin matar sun ce 'yan kungiyar Al-shabab ne suka bi ta har gida, kana suka bukace ta da ta sanya hijabi, amma daga baya da suka sake komawa gidanta sai suka tarar da ita babu hijabi, nan take suka harbe ta.

Sai dai kungiyar Alshabab din ta musanta cewa mutanenta ne suka kashe matar, saboda a cewar kungiyar ba ta da cikakken iko a kan yankin da matar take.

Kungiyar Al-shabab dai ita ce ke da iko da mafi yawan kudanci da kuma tsakiyar Somalia, kuma tana tilasta wa mutane irin sutarar da suke sanyawa.

Karin bayani