An jefa bam cikin massallaci a Yobe

Image caption Hari na biyu dai na kunar bakin wake ne.

Rahotanni daga jihar Yoben Najeriya na cewa wasu hare-haren bam da aka kai kan wani masallaci da wani wurin zaman jama'a sun hallaka akalla mutane goma.

Mutane biyar ne suka mutu wasu kuma kusan talatin suka samu raunuka a harin farko wanda aka kai kan masallacin Alkali Imam Kalli da ke garin Potiskum lokacin da ake sallar Isha'i.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa wani mutum ne ya tsaya da mota ya wurga bam din saannan ya arce da marecen ranar Talata.

Hari na biyu kuwa wanda aka ce an kai kan wani wurin zaman jama'a a garin na Potiskum, ya hallaka mutane biyar ciki har da wanda ya kai harin, tare da raunata wasu mutane hudu.

Har yanzu hukumomin Najeriya ba su ce uffan ba dangane da hare-haren.

Karin bayani