WHO ta kaddamar da shiri kan cutar Ebola

Cutar Ebola
Image caption Cutar Ebola

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta kaddamar da wani shiri na dala miliyan 100 domin yaki da yaduwar cutar Ebola a Yammacin Afirka.

Masana kimiyya sun gano kwayar cutar ce tun shekarun 1970, amma har yanzu ba ta da magani.

Hukumomin Nigeria sun ce suna ci gaba da daukan matakan kaucewa yaduwar cutar, tun bayan da wani dan kasar Liberia da ya shigo dauke da ita ya mutu.

Ministan Lafiya na kasar Farfesa Onyebuchi Chuckwu, ya ce yanzu haka mutane 69 ne aka sawa ido don ganin ko suna dauke da cutar kana an kebe mutane biyu.

Hukumar WHO dai ta shawarci al'ummomi da su killace marasa lafiya, da binne wadanda suka rasu nan take.

An gano cutar ce a wacce bata da magani a shekara ta1976 tana da matukar hadari, amma kuma tana da iyaka.