An kashe mutane 10 a Taraba

Hakkin mallakar hoto google
Image caption An tura karin jami'an tsaro a Ibi

Rahotanni daga garin Ibi na jihar Taraba na cewa akalla mutane 10 sun rasu a wani tashin hankali mai nasaba da kabilanci da addini tsakanin Hausawa da Fulani a bangare guda, da kuma 'yan kabilar Jukun a daya bangaren.

Tuni dai aka tura karin jami'an tsaro masu sintiri domin kwantar da tarzomar.

Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana kama mutane kimanin 14 da ake zargi da hannu a rigimar suna kuma dauke da muggan makamai.

Rahotanni sun ce an fara rikicin ne tun da misalin karfe hudu na asubahin ranar Alhamis.

Abdulrashid Usman Ajiya, shugaban matasa na Hausa Fulani a karamar hukumar Ibi, ya zargi 'yan kabilar Jukun da kai masu hari da kuma shigo da wasu sojan haya daga wajen yankin.

Amma tsohon shugaban matasan kabilar Jukun a yankin na Ibi, Mista Jonah Azongwa, ya musanta zargin cewa sune suka fara kai farmaki, kana ya yi zargin cewa harbin ya soma fitowa ne daga bangaren Hausawa.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana yawan samun rikicin kabilanci a Taraba

Rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba ta bayyana cewa tashin hankalin ya soma ne ranar Laraba da yamma yayin da wasu mazauna garin Ibi suka je garin Wukari mai makwabtaka suka cire kudi daga asusunsu na bankin sai wasu matasa masu dauke da makamai suka far musu a kan hanyarsu ta komawa Ibi.

Sannan suka kwace kudin kimanin naira dubu dari biyu, lamarin kuma ya haifar da zaman dardar a cikin garin Ibi abin da ya sanya da safiyar ranar Alhamis lamura suka kara dagulewa.

Yankin na Ibi da ma Wukari da ke jihar ta Taraba dai sun dade suna fama da ringingimu masu nasaba da kabilanci da addini.

Karin bayani