'Cikas a yunkurin kawar da Malaria'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Zazzabin cizon sauro na hallaka dubban mutane a duniya

Kwararrun masu bincike sun yi gargadin cewa, kwayoyin cutar zazzabin cizon sauro da ke bijirewa magani sun yadu, a yankunan kan iyakar kudu maso gabashin Asia, inda suke barazana sosai ga kokarin yaki da cutar ta Malaria.

A gwajin da aka gudanar a kan marassa lafiya sama da dubu daya, a yankunan kasar Cambodia da Burma ko Myanmar da Thailand da Vietnam, an gano kwayar cutar wadda ke bijirewa daya daga cikin magungunan Malaria mafi tasiri, wato Artemisinin.

Rahoton wanda aka wallafa a mujallar harkokin lafiya ta New England da ke Amurka, ya ce rubanya yawan maganin da ake baiwa marasa lafiya ga wanda ya kamu da ita da farko, zai iya taimakawa wajen, yaki da bazuwar kwayar cutar a kasashen Asia da Afrika, sai dai kuma akwai matsalar karancin lokaci.

Dubun dubatar mutane ne dai ke mutuwa a sanadiyyar kamuwa da cutar zazzabin cizon sauron kowa ce shekara a Afrika.

Karin bayani