Za'a tara dala miliyan 100 dan yakar Ebola

Cutar Ebola Hakkin mallakar hoto
Image caption Kawo yanzu dai cutar Ebola ba ta da magani.

Shugabannin kasashen yammacin Africa da ke fama da cutar Ebola za su hadu da hukumar lafiya ta duniya WHO a Guinea.

Taron na kwana guda zai kaddamar da tallafin dala miliyan dari domin yakar cutar Ebola da ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da dari bakwai a kasashen Guinea, da Liberia da kuma Salo daga watan Fabrairu wannan shekara zuwa yanzu.

Poul Garwood shi ne kakakin Hukumar lafiya ta duniya, ya kuma bayyana yadda shirin zai kasance.

Inda Yace wannan shiri ya kunshi samar da ma'aikatan lafiya da za su taimaka wato likitoci, da ma'aikatan jiyya da kwararrun masu binciken lafiya, da samar da mutanen da za su yi aiki da shugabannin al'umma dan wayar da kan jama'a akan matakin farko da ya mata a dauka idan cutar ta bullo.