Isra'ila da Hamas za su tsagaita wuta

Hare-haren Isra'ila a Gaza Hakkin mallakar hoto
Image caption Hare-haren Isra'ila a Gaza

Isra'Ila da mayakan Plasdinawa na kungiyar Hamas sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 72 a zirin Gaza wadda za ta fara aiki a yau juma'a.

Hamas dai ta Ce za ta ajiye makamanta kamar yadda Majalisar Dunkin Duniya ta bukata, yayinda Israela tace dakarun ta za su ci gaba da kai hare-hare a hanyoyi na karkashin kasa a lokacin yarjejeniyar.

Fadar White House ta bukaci dukkan bangarorin biyu su takaita matakan da suke dauka a lokacin yarjejeniyar, kana kuma su gaggauta zama a teburin sulhu don kawo karshen rikicin.

Wakilin BBC ya bayyana cewa yankunan na fuskantar munanan hare-hare.

A bangare guda kuma dukkan bangarorin biyu na fuskantar matsin lambar don kawo karshen gabar da suke da juna, bayan shafe makonni 3 ana fafatawar da ta dai-dai-ta Gaza.

Fiye da Plasdinawa 1400 ne suka rasa rayukansu yawancinsu fararen hula kananan yara, yayinda wasu dubbai suka bar muhallinsu.

Karin bayani