Kadangaren Dinosaurs mai gashi na yaduwa

Nau'in kadangaren Dinosaurs mai gashi a jikinsa
Image caption wannan nau'i na Dinosaurs ya na da gashi a jikinsa, da dogayen kafafu, masu dauke da farata zako-zako

Wani binciken kimiyya ya gano cewa dukkan jikin kadangarun Dinosaurs na da gashi a jikinsu, ko kuma gashin zai iya fitowa a jikinsu.

An gano hakan ne a jikin kashin wani kadangaren Dinosaurs mai shekaru miliyan 150 a Siberia, wanda ya bayyana cewa ana iya samun kadangaren mai gashi a jikinsa fiye da yadda aka yi tsammani a baya.

Jagoran binciken ya shaidawa BBC cewa, sabon binciken da suka gudanar ya sauya baki dayan tunaninsu akan kadangaren na Dinosaurs.

An dai wallafa wannan bincike ne a jaridar mujallar Science.

Kadangaren Dinosaurs da aka yi binciken akan sa mai suna Kulindadromeus Zabaikalius ya na da tsahon mita 1, da dan gajeren hanci, da kuma dogayen kafafu, da gajerun kafada ka na kuma da farata guda biyar masu karfin gaske.

Hakoran sa kuma ya nuna yadda ya ke da karfin cin tsirrai.

Kawo yanzu dai an gano irin wannan kadangaren Dinosaurs mai gashi a jikinsa ne a kasar China, daga dabbobin da suke cin nama wadanda ake kira Theropods a turance.

Bincike na baya-bayan anan da aak gudanar a kasar Rasha, an gano shi ne daga a wurin kadangarun Dinosaurs da aka killace wadanda ba sa cin komai sai tsirrai, wanda hakan yake a kusan dukkannin kadangaru irinsu.