Cutar amai da gudawa a Damboa

'Yan gudun hijira a Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption 'Yan gudun hijira a Nijeriya

A Najeriya Hukumar ba da agajin gaggawa wato NEMA ta ce ta soma daukar matakai wajen hana yaduwar cutar amai da gudawa da ta barke a sansanin 'yan gudun hijira mazauna Damboa dake garin Biu a jahar Borno.

Mutane hudu ne aka ba da rahotan cewa sun mutu a sansanin ba ya ga mutane sama da 100 da suka kamu da cutar.

Alhaji Muhammadu Kanal jami'i a hukumar ta NEMA dake kula da shiyyar arewa maso gabashin Najeriya ya ce yawan mutane da rashin tsafta ne suka haddasa barkewar annobar.

Jami'in yace hakan ya faru ne duk da fadakarwa da aka yi musu ta yiwuwar fuskantar wannan yanayin. Kodayake yace, a dalilin fadakarwar ne lamarin ya zoi da sauki.

Karin bayani