Boko Haram: An kaddamar da gidauniya

Hare-haren 'yan Boko Haram
Image caption Hare-haren 'yan Boko Haram

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da gidauniyar tara kudi domin tallafa wa al'ummomin da hare-haren kungiyar Boko Haram da sauran ayyukan ta'addanci suka dai-daita a wasu sassan kasar.

Gwamnatin Nijeriyar dai tana son ganin an tara Dala Miliyan Dari Biyar domin tallafawa wadanda hare haren 'yan Boko Haram din ya shafa cikin shekara guda.

To ko yaya wasu mazauna irin wadannan yankuna suka ji da irin wannan mataki da gwamnati take shirin dauka, sannan ko ta wacce hanya suke son ganin ya kamata abi wajen amfani da irin wadannan kudade da ake son tarawa ?

Wasu mazauna Borno da suka bayyana ra'ayinsu, sun ce domin taimakon ya kai gare su, kamata ya yi a cikin kwamitin da za a nada, a sanya wasu wakilansu, domin su ne suka san su, kuma suka san bukatunsu da irin hasarar da suka yi.

Karin bayani