Niger ta samu tallafin CFA biliyan shida

Image caption Dubban 'yan Niger na fama da yunwa

A Jamhuriyar Niger asusun agajin gaggawa na majalisar dinkin duniya CERF ya bayar da gudumawar CFA biliyan 6 don tallafawa 'yan gudun hijirar Nigeria a cikin kasar.

Daga cikin kudin tallafi wasu za a kashe kan da samar da abinci ga sauran masu dan karamin karfi a Niger.

Hakan ya biyo bayan kiraye-kirayen da gwamnatin ta Niger ta yi ga abokan arziki domin samun taimakon da za ta kula da matsalar abincin da wasu miliyoyin 'yan kasar gami da 'yan gudun hijiran wasu kasashe makwabta.

Dubban 'yan Nigeria sun tallaka Niger sakamakon rikicin Boko Haram a arewacin kasar.