Suleiman Abba ya zama sabon Sufeto Janar

Image caption 'Yan sandan Nigeria na fuskantar kalubalen tsaro

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya nada Suleiman Abba a matsayin sabon mukadashin sufeto Janar na 'yan sandan kasar.

Sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ce Mr Abba zai kama aiki ne daga 1 ga watan Agustan 2014.

Suleiman Abba ya maye gurbin Muhammed Abubakar wanda ya kamalla shekaru 35 da doka ta tanadar na aikin 'yan sanda.

Kafin nadin, AIG Sulaiman Abba, shi ne ke rike mukamin mataimakin sufeton 'yan sanda mai kula da shiyya ta 7 da suka hada da Abuja da jahohin Kaduna da Niger.

Karin bayani