An soke dokar luwadi a Uganda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan luwadi sun yi murnar hukuncin kotun

Kotun tsarin mulki ta Uganda ta soke wata doka da ake ta cece kuce a kanta da ke nuna kyama ga masu auren jinsi daya.

Dokar ta karfafa dokokin hukunta masu yin luwadi ko madigo.

Alkalin kotun ya ce an soke dokar saboda majalissar dokokin kasar ta amince da ita ne ba tare da samun yawan 'yan majalissun da suka kamata ba.

Dama dai Luwadi abune da ya sabawa doka a Uganda, to amma dokar wadda ta fara aiki a watan Fabrairu ta maida duk wani mataki na yayata shi ya zama laifi.

Sannan a karon farko ta hada da madigo a karkashin dokar, kuma duk wanda yayi aure na jinsi daya ko luwadi ko madigo zai gamu da daurin rai da rai.

Karin bayani