Isra'ila ta ce za ta cigaba da kare al'ummarta

Benjamin Netanyahu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Netanyahu ya ce Isra'ila za ta cigaba da farmaki a Gaza

Fira ministan Israi'la Benyamin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta cigaba da farmakin da ta ke kaiwa a Gaza har sai ta dawo da yanayin cikakken tsaro kamar yadda ta yiwa al'ummar kasar alkawari.

Da yake jawabi wajen wani taron manema labarai a Israi'la, Mr Netanyahu ya ce sojoji za su cigaba da fafata yaki domin dakatar da hare-hare daga Hamas koda kuwa bayan Isra'ila ta kammala aikin lalata dukkanin hanyoyin karkashin kasa.

Jami'an kiwon lafiya a Gaza dai sun ce Falasdinawa 200 ne suka rasu a hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama tun bayan da takaitacciyar 'yarjejeniyar tsagaida bude wuta ta ruguje a jiya.

Hari mafi muni ya faru a Rafah inda anan ne Isra'ila ta ce an sace sojan ta Hadar Goldin, a jiya.

A halin da ake ciki kuma, ana cigaba da kokarin sulhunta rikicin na Palasdinawa da Isra'ila a Masar.

Sai dai fatan da ake da shi na samun wani cigaba ba mai yawa ba ne saboda bisa dukkan alamu Isra'ila ba ta tura wakilai wajen tattaunawar ba.

Karin bayani