Najeriya ta hana a shigo da gawaki

Labarin mutuwar wani dan Liberia a Lagos Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yanzu haka akwai gawaki biyu da aka dauko daga Liberia da Saliyo

Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin dakatar da dauko gawakin mutane daga kasashen da cutar Ebola ta shafa zuwa cikin kasar, a wani mataki na hana yaduwar cutar cikin Najeriya.

Hukumomi sun ce sun dauki mataki ne saboda kwayar cutar ta Ebola tana yaduwa ne daga jikin mamaci fiye da rayayye.

Farfesa Abdulsalam Nasidi, Direkta a Cibiyar kare yaduwar cututtuka a Najeriya, ya shaidawa BBC cewa yanzu haka akwai gawaki biyu da aka shigo da su Najeriya daga Liberia da kuma Saliyo, saboda haka idan baa tsaida hakan ba, to duk yunkurin da ake yi na hana yaduwar cutar a Najeriya zai ci tura.

Ya kuma tabbatar cewa bayan ga dan Liberian nan da ya mutu a Lagos a sakamakon cutar ta Ebola, har yanzu baa sake samun wasu karin mutane da ke dauke da kwayar cutar ba.

Cutar Ebola dai ta hallaka sama da mutane fiye da 700 zuwa yanzu a kasashen Liberia da Guinea da kuma Saliyo.

Karin bayani