Ban Ki-Moon ya yi Allawadai da harin Gaza

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon Hakkin mallakar hoto
Image caption Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon

Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya bayyana harin makami mai linzami da aka kai akan wata makarantar dake karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya a Gaza da cewa ya sabawa da'a ta kamalar hankali kuma bakar aniya ce ta mummunan laifi.

Amurka ta ce ta kadu da luguden bama baman tana mai cewa abin kunya ne.

Falasdinawa sun ce akalla mutane goma sun mutu a harin.

Israila ta ce ta hari wasu mayakan jihadin Islama ne su ukku wadanda ke tafiya akan babur kusa da makarantar ta Majalisar Dinkin Duniya amma tana gudanar da binciken ta'adin da harin ya haifar.

Wani jami'in hukumar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin Falasdinawa ya shaidawa BBC cewa halin da ake ciki a Gaza ya yi muni matuka.

Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da ake tattaunawar kawo karshen rikicin a birnin Al-kahira na kasar Masar.

A daya bangaren kuma, anyi jana'izar Hadar Goldin sojan kasar da a baya aka ce 'yan Hamas ne suka sace shi.

Yanzu dai ta tabbata cewa ya mutu ne a fadan.

Karin bayani