An kashe mutane akalla goma a Gaza

Hakkin mallakar hoto AFP

Rohotanni daga Falastinu na cewa wani hari da Isra'ila ta kai ta sama a kusa da wata makarantar dake karkashin ikon Majalisar Dinkin Duniya da jama'a ke neman mafaka a cikinta ya hallaka a kalla mutane goma.

Harin na zuwa ne a dai dai lokacin da ake tattaunawar kawo karshen rikicin a birnin Al-kahira na kasar Masar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya yi Allawadai da harin, yana mai bayyana shi da cewa wani "mugun abune."

Ganau sun ce wata roka da Isra'ila ta harba ne ya fada akan makarantar, inda dubban jama'a ke neman mafaka.

A daya bangaren kuma, anyi jana'izar Hadar Goldin sojan kasar da a baya aka ce 'yan Hamas ne suka sace shi.

Yanzu dai ta tabbata cewa ya mutu ne a fadan.