An saci bayanan na'urar Israela.

Na'urar kakkabo makaman roka wato Irone Dome Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Israela na amfani da na'urar ne domin kare fararen hular ta a yakin da ta ke fafatawa da mayakan Hamas na Falasdinawa

BBC ta gano wasu shaidu da suka tabbatar da cewa masu satar bayanai ta internet sun saci wasu bayanan soji na sirri daga wasu manyan kamfanonin gwamnati guda biyu da ke samar da na'urar kakkabo makaman roka da Hams ke harbawa Israela.

Wannan bayanan dai wani mai rubuce-rubuce kan harkokin tsaro mai suna Brian Krebs ya wallafa a ranar litinin.

Sai dai kamfanonin biyu sun musanta cewa an saci wadannan bayanai na sirri.

Haka kuma masu binciken da suka gano wannan lamari sun bawa BBC damar duba wani bincike na kwararru masu binciken sirri, wanda ya nuna cewa an kwashe bayanan sirri na sojojin Israela kusan na takardu fiye da dari.

Bayanan da aka shafe watanni ana sata sun hadar da;

*Bayanan Makamai masu linzami na Arrow 3 a turance.

*Bayanan Motocin yaki marasa matuka wato Drone a turance.

*Da kuma bayanan makaraman roka.

Kamfanin Cyber Engeneering Service su ne suka fara gano ayyukan masu satar bayanan sirrin ta Internet cikin watanni 8, kuma tsakanin shekarar 20011 zuwa 20012.

Sun bayyana cewa bayanan da aka sata, su na da nasaba da na'urar kakkabo makaman roka jo Iron Dome a turance.

Ita dai na'urar Iron Dome amfaninta shi ne kakkabo makaman rokar ad Hamas ke harbawa Israela.

An bayyana cewa wannan na'ura ta kakkabo makaman Roka da Hams din ke harbawa Isarela ta taimaka sosai wajen fararen hular Israela a yakin da suke fafatawa da mayakan Hamas na Falasdinawa a zirin Gaza.