Somalia ta kashe 'yan Al Shabbab

'Yan kungiyar Al Shabbab a Somaliya
Image caption 'Yan kungiyar Al Shabbab a Somaliya

A Somalia an aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar harbe wa da bindiga akan wasu yan kungiyar Al Shabbab su uku a Mogadishu babban birnin kasar.

Yan sanda sun ce daya daga cikin mutanen yana cikin wadanda suka kai hari fadar shugaban kasar a watan da ya gabata, inda suka bude wuta da kuma tada wata nakiya da suka dasa a cikin wata karamar mota.

Dukkan mutanen uku wadanda aka yanke musu hukuncin kisa an harbe su ne a gaban manyan jami'an soji a makarantar horar da jami'an yan sanda dake Mogadishu.

Karin bayani