An sake gano gawawwaki MH17 a Ukraine

Masu binciken jirgin MH17 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana ci gaba da gwabzawa tsakanin sojin gwamnati Ukraine da 'yan tawaye a inda jirgin ya fadi.

Masu bincike na kasashen waje tare da karnukan bincike sun gano wasu karin gawawwaki da tarkacen mutanen cikin jirgin Malaysian nan mai dauke da pasinjoji 298 da aka harbo fiye da makwanni biyu da suka wuce.

Jagoran masu binciken Pieter-jaap Aalbersberg ya shaidawa manema labarai a Kiev cewa kwararru saba'in da biyu sun yi bincike a wurin amma ba su samo komai ba.

An ci gaba da bata-kashi a kusa da inda jirgin ya fado tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan tawayen da ake zargi da alhakin kakkabo jirgin mai lamba MH17.

Kakakin masu sanya idanu na kasashen waje Alexander Hug ya bayyana cewa babu tabbacin ko za su kammala binciken da suke yi a wajen, saboda makaman Atilari ake harbowa.