Taron koli na Amurka da Afrika

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Kasashen Sudan da Zambabwe sun bayyana takaicinsu na rashin gayyatar shugabannin kasashen biyu da Amurka taki yizuwa taro kwanaki uku na musamman da aka shiryawa shugabanni kasashen Afirka wanda ke gudana a Washington.

Ministan harkokin wajen Sudan ya ce, taron ba tare da shugaba Omar al-Bashir ba, ba zai yi armashi ba.

Shi ma ministan harkokin wajen Zimbabwe cewa ya yi, shawarar kin gayyatar shugaba Robert Mugabe bai yi dadi ba duba da irin kokarin da kasar ke yi na inganta alaka da Amurka.

Haka nan shugabannin kasashen Eritrea da Afrika ta tsakiya ba a basu goron gayyata ba.

Akalla shugabanni 50 ke halartar taron in banda na Liberia da Sierra Leone da suka zabi zama a kasashen nasu saboda matsalar cutar Ebola da suke fama da ita.

Za a gudanar da gangamin kungiyoyin fararen hula, sannan za a gudanar da Tattaunawar harkokin kasuwanci ranar Talata.

Bugu da kari kuma Shugabannin kasashe da kuma Prime Ministocin Kasashe za su gudanar da Tattaunawa a ranar Laraba.

Karin bayani