Isra'ila ta ci gaba da kai farmaki a Gaza

Zirin Gaza
Image caption Zirin Gaza

Dakarun Isra'ila sun ci gaba da kai hari kan Gaza, bayan da aka kawo karshen tsagaita wutar jin kai.

Pira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce za a ci gaba da kai harin har sai an dawo da kwanciyar hankali da tsaro a Isra'ilar.

Palasdinawan dai na zargin Isra'ila da karya yarjejeniyar tsagaita wutar, bayanda ta kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira dake arewacin Gaza, da ya hallaka wata mata da yarinya 'yar shekara 8.

Ita ma dai Isra'ilar ta ce mayakan Hamas sun ci gaba da harba rokoki a kasarta.

Wani mazaunin Gaza, Atef Abu Saif ya shaidawa BBC cewa Palasdinawa da dama dake zaune a birnin na fatan wataran komai zai daidaita.

Ya ce "Ina ga daga karshe dole rayuwa ta ci gaba, ka yarda cewa idan babu fata na gari baza ka taba rayuwa ba."

A karon farko shugaban Faransa Francois Hollande,ya soki Isra'ila kan abinda ya ce kisan kiyashin da take yi wa Palasdinawa fararen hula a Gaza.

Shugaba Hollande ya kwatanta yanayin da irin gallazawar da ake yiwa Kiristoci a Iraqi, da kuma gallazawar da ake yiwa kananan kabilu a Syria.

Karin bayani