MNSD ta tabbatar da kamen jami'an ta

'Yan adawan Nijer Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan adawan Nijer

A jamhuriyar Nijar jam'iyyar MNSD Nasara mai adawa ta tabbatar da kama wasu daga cikin shugabanninta da suka hada da mataimakin sakatare janar na jam'iyyar malam Umaru Hadari da shugaban jam'iyyar reshen jahar Damagaram.

Rahotanni kuma sun nuna cewa a yanzu haka jami'an tsaro na neman wasu manya manyan jami'an jam'iyyar.

Sai dai ya zuwa yanzu hukumomin jahar ta Damagaram ba su yi wani Karin haske ba dangane da zargin da suke yi ma shugabannin jam'iyyar ta MNSD.

Akwai dai alamu dake nuna cewa kamun na su, ba zai rasa nasaba ba da taron da suka shirya a Damagaram a ranar asabar din da ta gabata ba, taron da hukumomin jahar suka hana.

Karin bayani