Ana ci gaba da ceton mutane a China

Ma'ikatan ceto da ke kokarin zakulo wadanda abin ya shafa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Fiye da mutane dari uku girgizar kasar ta rutsa da su a yankin Yunnan.

Ma'aikatan ceto na ci gaba da fafutukar isa inda girgizar kasa ta shafa yankin Yunnan na kasar China a jiya lahadi, inda ta yi sanadiyyar rasa rayukan fiye da mutane 300.

Ma'aikatan gaggawa na kokarin gyaran hanyoyin da baraguzan gini suka mamaye, domin samun damar isa wuraren da lamarin ya yin da ake tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Dubban mutanen da lamarin ya rutsa da su dai ma'aikatan ceto sun gagara isa inda suke.

Wani mutum ya shiadawa BBC cewa kashi 2 cikin 3 na gidadajen kauyensu baki daya sun ruguje.

A bangare guda kuma an kai kayayyakin agaji da suka shafi dubban gadaje da kuma tantuna ga wadanda abin ya rutsa da su.

Wani likita ya shaidawa BBC cewa ma'aikatansa da tanti suka yi asibitin wucin gadi a Yunnan domin kula da marasa lafiya.

Ya kuma kara da cewa a lokacin da suka isa yankin, ko ina gawawwaki ne a yashe akan hanya da mutanen da suka jikkata.