Taron koli na Amurka da Afrika

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugabannin Afirka na hallara a birnin Washington na Amurka domin halartar wani Taron koli da Shugaba Barack Obama.

An gayyaci Kasashe 50 a wannan taro wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Amurkar.

Abubuwan da za su wakana yau Litinin sun hada da gangamin kungiyoyin fararen hula, sannan za a gudanar da Tattaunawar harkokin kasuwanci gobe Talata.

Bugu da kari kuma Shugabannin kasashe da kuma Prime Ministocin Kasashe za su gudanar da Tattaunawa a ranar Laraba.

Karin bayani