An bindige sojin Amurka a Afghanistan

Sojin Afghanistan a Kabul Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin Afghanistan a Kabul

Wani sojan Afghanistan ya bindige jami'in sojan Amurka tare da raunata karin wasu dakarun kasa da kasa da na Afghanistan a wani sansanin soji dake kusa da Kabul babban birnin kasar.

Mahukunta sun ce sojan ya bude wuta ne daga inda yake gadin mashigin sansanin, inda shima daga bisani aka bindige shi.

Ma'iakatar harkokin tsaro ta Afghanistan ta shaidawa BBC cewa shekaru uku da suka gabata ne aka dauke shi aiki.

Yayinda yake magana daga ma'aikar tsaro ta Pentagon Rear Admiral John Kirby ya shaidawa manema labarai cewa ba za a iya kaucewa hari daga dan cikin gida ba.

Karin bayani