An wanke gwamna Al-Makura, sai dai...

Hakkin mallakar hoto website nassarawa
Image caption Ana zargin gwamnan da aikata laifuka 16

Kwamitin da majalisar dokokin jihar Nasarawa a Nigeria ta sa aka kafa domin binciken gwamnan jihar Tanko Al-Makura ya yi watsi da zargin da ake wa gwamnan, amma 'yan majalisar sun ki yarda.

Kwamitin na mutum bakwai wanda babban mai shari'ar jihar Umaru Dikko ya kafa ya kammala zamansa a ranar Talata, inda ya yi watsi da zargin almundahana da ake wa gwamnan, abin da ke nuna cewa yunkurin tsige shi bai yi nasara ba.

Mai tsawatarwa na Majalisar dokokin Jihar Nasarawan, Muhammad Okpede, ya ce ba su samu rahoton kwamitin game da wanke gwamnan ba.

Wani kwamitin lauyoyi da majalisar ta kafa ya halarci zaman kwamitin na ranar Talata, inda ya shaida wa kwamitin binciken Al-Makuran cewa ba su yarda da zamansa ba.