Dell zai yi fasahar gano yanayin mutum

Hakkin mallakar hoto dell
Image caption Shugaban bincike na kamfanin na da kwarin guiwa kan aikin

Kamfanin kera kwamfuta na Dell na shirin samar da fasahar nazarin yanayin halin da mutum ke ciki.

Kamfanin ya ce a yanzu haka wasu kwararrun ma'aikatansa biyu na aiki a kan fasahar.

Kuma kamfanin yana sa ran nan da shekara ta 2017 za a kammala aikin.

Shugaban sashen sabbin bincike na kamfanin, Jai Menon ya gaya wa BBC cewa, Dell, na aikin samar da fasahar wadda za ta fahimci yanayin halin da mutum ke ciki.

Shugaban binciken ya ce za a iya amfani da fasahar a ofis ko kuma wurin wasa.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Za dai a rika sanya na'urar fasahar ne a ka, inda za ta rika bayar da bayani a kan wanda ya daura ta.

Sai dai kuma wasu masana na nuna shakku akan wannan aiki.

Kamar yadda wani malamin jami'a ya ce, gane yanayin da mutum ke ciki abu ne mai wuyar gaske.

Wani masanin kuma ya ce, ko da na'urar ta kasance mai bayar da ingantattun bayanai, akwai yuwuwar ma'aikata da dama za su ki amincewa da sakamakon.