Google ya cire wasannin fadan Gaza

Hakkin mallakar hoto gamytech
Image caption Kungiyar Amnesty International ma ta ce wasannin kwanfutar ba su dace ba

Kamfanin Google ya fitar da wasu wasannin kwamfuta na yakin Israela da Hamas daga rumbun Android.

Kamfanin na Amurka ya cire wani wasan bidiyo da ake kira Rocket Pride.

A wasan dai masu yin shi, su kan yi yunkurin kauce wa na'urar kare hare haren sama da ake kai wa Israela.

Haka kuma kamfanin na Google ya cire wasan Iron Dome, na Gamytech, wanda ke kalubalantar masu wasan, su kare rokokin da Hamas ke harbawa.

Sai dai kuma kamfanin ya bar sauran nau'ukan wasannin bidiyon da ba a ayyana wani a matsayin abokin gaba ba a rumbun na Google na app store.

Hakkin mallakar hoto best arabic games

Daman tun da farko masu raji sun soki bullo da wasannin kwamfutar na fadan Israela da Hamas.

A cewar shugaban kungiyar Yahudawa a Amurka, Morton Klein, daman wasannin ba su dace ba, kuma suna da hadari.

Ya ce, rashin dacewar kuwa shi ne, a rika daukaka kisan da Israela ke yi wa larabawa.

Ko kuma a daukaka kisan da larabawa ke yi wa Yahudawa.