An sake samun tsaiko a tattaunawar Sudan ta Kudu

Sansanin 'yan gudun hijira
Image caption Sansanin 'yan gudun hijira

Yunkurin dawo da zaman lafiya a Sudan ta Kudu ya sake gamuwa da cikas, sa'oi 24 da fara shi.

Masu shiga tsakani daga kungiyar kasashen gabashin Afrika, IGAD, sun bayyana cewa, bangaren 'yan tawaye, ya ki halartar zaman sasantawar a rana ta biyu, wanda ake yi a, babban birnin Ethiopia ko Habasha, wato Addis Ababa.

Kungiyar ta IGAD , har ila yau ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa lamba ga 'yan tawayen domin su dawo teburin sulhu.

Ana ci gaba da fada a Sudan ta Kudun duk da kokarin da aka yi a baya na tabbatar da zaman lafiya.

Sama da mutane miliyan daya da rabi ne rikicin ya raba da muhallansu tun lokacin da aka fara shi, a karshen shekarar da ta wuce.