Boko Haram: Mutane 650,000 sun rabu da muhallansu

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Mata da kananan yara da dama ne ke cikin wadanda suka rabu da gidajensu saboda hare-haren Boko Haram

Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa sun raba mutane kusan 650,000 da gidajensu a Najeriya.

Wato an samu karuwar mutanen da suka yi hijira da kusan 200,000 a yankin arewa-maso-gabashin kasar tun daga watan Mayu.

Hukumar ta ce 436,608 daga cikin mutanen sun kauracewa gidajensu ne a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe da ke karkashin dokar ta-baci.

Haka kuma wasu mutane 210,085 sun ketara zuwa jihohin da ke makwabtaka da wadannan jihohi uku, yayin da wasu dubban mutanen kuma suka ketara zuwa kasashen Kamaru da Chadi da kuma Nijar.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba