Mece ce cutar Ebola?

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ya zuwa yanzu cutar Ebola da ta barke a yankin Afirka ta yamma ita ce cuta mafi hatsari a duniya, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce ya zuwa ranar 4 ga watan Agusta cutar ta kashe mutane 932, yayin da wasu mutane 1,711 kuma suka harbu da cutar a kasashen Guinea, Liberia da Nigeria da kuma Saliyo.

Shin mece ce Ebola?

Ebola wata kwayar cutar virus ce wadda alamun kamuwa da ita na farko suka hada da zazzabi mai zafi da ya wuce kima da kasala mai karfi da ciwon gabobi da rikewar makogwaro a cewa Hukumar lafiya ta duniya.

Sai matakin cutar na gaba wato amai da gudawa da kuma a wasu lokuta, zubar jini a ciki da kuma jiki.

Cutar Ebola na yaduwa a tsakanin mutane ta hanyar ta'ammali da dabbobin da suka kamu da cutar irinsu gwaggon Biri da Jemage da Gada.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Daga nan sai ta yadu tsakanin mutane ta hanyar jini da danshin jiki ko na gabobin jiki ko kuma ta hanyar dauka daga muhallan da suka gurbata.

Hatta jana'izar gawar mai Ebola tana iya zama hatsari, idan masu makoki suka taba jikin mamacin.

Kwayoyin cutar kan dauki tsawon kwana biyu zuwa makonni uku kafin su kyankyashe, kuma kula da wadanda suka kamu da cutar abu ne mai wuya.

Ma'aikatan lafiya suna cikin hatsari idan suka duba lafiyar wanda ya kamu, ba tare da daukar matakan kariyan da suka dace ba.

Ya zuwa yanzu cutar Ebola a jikin Mutane ta takaita akasari ga nahiyar Afirka, ko da yake an samu bullar wani nau'inta a kasar Philippines.

Mutane za su iya yada ta matukar jininsu ko wani nau'in sinadarin jiki ya shafi wasu mutane, a wasu lokuta har bayan fiye da makonni bakwai da samun waraka.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Asalin Ebola

An fara gano cutar ne a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo cikin shekarar 1976 tun lokacin ne ta ci gaba da yaduwa a tsakanin kasashen gabashin Afirka ciki har da Uganda da Sudan.

Cutar tana da bazata don kuwa ta bulla a kasar Guinea a watan Fabairu, wadda ba ta taba saninta ba a baya, inda take ci gaba da yaduwa a birane.

An killace wani mutum dan Liberia da ya je Lagos a Najeriya a cikin watan Yuli, kuma daga bisani Ebola ta yi sanadin mutuwarsa, bullar cutar ta farko kenan a Najeriyar.

Tun daga nan ne daya daga cikin likitoci da ma'aikatan jinyar da suka kula da shi suka kamu, hukumin kasar sun kuma tabbatar da mutuwar wata jami'ar a cikinsu, wadda ita ce 'yar Najeriya ta farko da ta mutu sakamakon cutar, yayin da kuma aka kebe wasu mutane takwas a jihar Lagos, kuma biyar daga cikinsu an tabbatar suna dauke da cutar.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Ta yaya za a kare kai?

Hukumar lafiya ta duniya ta ba da shawarar cewa a kauce wa mu'amala da masu cutar Ebola da kuma taba sinadarin danshin jikinsu.

Kada a yi amfani da komai irinsu tawul da ya gurbata.

Kamata ya yi masu kula da mutanen da suka kamu da Ebola su sanya safar hannu da kayayyakin kare-kai, irinsu abin rufe fuska kuma a dinga wanke hannu a ko da yaushe.