Ebola: Kasashe na daukar matakan kariya

Hakkin mallakar hoto Getty

Kasar Girka ta bai wa 'yan kasarta shawarar kada su yi tafiya zuwa kasashen Najeriya da Saliyo da Liberia da kuma Guinea, kasashen da aka tabbatar da bullar cutar a Afirka.

Kasar Girka dai babbar hanya ce ta shiga kasashen Turai ga 'yan ci-rani daga Afirka da Asiya, ta ce za ta dauki karin matakai a kafofin shigarta sakamakon barkewar wannan cuta a Afirka ta yamma.

Ita ma Jamus wadda ta bayyana wa 'yan kasarta cewa babu shamaki ga wannan cuta mai saurin yaduwa ta ba su shawarar su guji tafiya zuwa kasashen Guinea, Liberiya da Saliyo saboda cutar ta Ebola,

Indiya ma ta dauki matakan tantancewa tare da bankado Fasinjojin jiragen sama da suka fito daga kasashen da ke fama da cutar, kana ta shawarci 'yan kasarta su raba kansu da zuwa yankin da cutar ta barke.

A cewar Hukumar lafiya ta duniya mutane 932 ne ya zuwa yanzu suka mutu sakamakon Ebola a Afirka ta yamma, kuma wasu mutanen 1,711 suka kamu da ita, tun lokacin da ta fara yaduwa a kasar Guinea cikin watan Fabrairu da ya wuce.