Ebola ta kashe jami'ar lafiya a Lagos

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikaciyar lafiyar ta kula da dan Liberiyan da ebola ta kashe a Lagos kuma an rufe asibitin

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar wata jami'ar lafiya a sanadiyar kamuwa da cutar Ebola a jihar Lagos.

Ministan lafiya na kasar, Onyebuchi Chukwu ya ce ma'aikaciyar ita ce 'yar Najeriya ta farko da cutar ta kashe.

Ma'aikaciyar na daga cikin jami'an lafiyar da suka kula da dan Liberiyan da ya kawo cutar Najeriya, Patrick Sawyer wanda shi ma ya mutu a jihar ta Lagos.

Jami'an lafiya sun tabbatar da karin wasu mutane biyar da ke dauke da cutar ta ebola kuma dukkansu ma'aikatan lafiya ne da suka kula da dan Liberiyan.

A halin yanzu dai mutane bakwai kenan aka tabbatar da sun harbu da cutar ebola, ciki har da jami'ar lafiyar da ta mutu da kuma Patrick Sawyer.

Ma'aikatar lafiya ta kasar dai ta ce akwai mutane 70 da ake sa ido a kansu, saboda mu'amalar da suka yi da wadanda ake zato ko aka tabbatar sun kamu da cutar ta Ebola.